<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Oh Duniya LW505</title>
<lyrics>[V1]
 KORUS
 Oh duniya, oh duniya, runfar kara take fa.
 Oh duniya, oh duniya, duniya mai shuɗewa.

[V2]
 1) Zaman duniya, zaman duniya, duniya sai iyawa.
 Ka jingina ga duniya, sai ƙarewa za ta yi.
 Korus

[V3]
 2) Ga masu bi na shan daɗi, sun manta da Allahnsu.
 Ba addu'a, ba wa'azi, ai Shaiɗan ya ɗaure su.
 Korus

[V4]
 3) Ga masu bi da arziki, sun maida shi Allahnsu.
 Ga masu bi sun sami illimi, sun maida shi Allahnsu.
 Korus

[V5]
 4) Ga masu bi, sun sami girma, sun maida shi Allahnsu.
 Ba addu'a ba wa'azi, ai Shaiɗan ya ɗaure su.
 Korus

[V6]
 5) Mu masu bi mu lura fa, ranan nan na zuwa fa.
 Mu farfaɗo mu yi addu'a, biyayya ce za mu yi.
 Korus

[V7]
 6) Kuɗi, girma, yabo, daɗi, ba za su cece mu ba.
 Nemi Allah ba shi girma, shi fa zai bada ceto.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>505</hymn_number>
</song>